1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Westerwelle na ziyara a yankin Gabas ta Tsakiya

May 18, 2013

A wannan Asabar Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle ke fara ziyara a yankin cin gashin kai na Palesdinu

https://p.dw.com/p/18aLB
epa03613566 German Foreign Minister Guido Westerwelle at the Friends of Yemen ministerial meeting in London, Britain, 07 March 2013. The conference aims to maintain international support and impetus for transition in Yemen based on the GCC 'Initiative and Implementation plan'. EPA/ANDY RAIN +++(c) dpa - Bildfunk+++ pixel
Hoto: picture-alliance/dpa

Yayin ziyarar zai gana da Firaminista Salam Fayyad a garin Ramallah na yankin Yamma da kogin Jordan. Wannan ziyara ta ministan harkokin wajen na Jamus wato Westerwelle tana zuwa ne bayan da a wannan Jumma'a ya gana da Firaministan Isira'ila Benjamin Netanyahu.

Tuni ministan ya nuna goyon baya ga shirin zaman lafiyar da Amirka ta gabatar, domin kawo karshen rikici tsakanin Isira'ila da Palesdinawa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas