Wen Jiabao na ci gaba da ziyara a nahiyar Afrika
June 20, 2006Talla
Praministan ƙasar Sin Wen Jiabao, na ci gaba da ziyara aiki a nahiyar Afrika.
Bayan ƙasashen Masar da Ghana, tun jiya ya fara rangadi a Congo, inda ya gana da shugaban ƙasar, bugu da ƙari shugaban ƙungiyar taraya Afrika Denis Sassou N´guesso.
A sakamakon wannan tantanawa,ƙasashen 2, sun rattaba hannu a kann yarjejeniyoyi daban-daban ta hanyar kasuwanci da kiwon lahia.
Sannan a yau, ya ziyarci babban asibitin Brazaville, kamin, ya sadu da ɗallibai na makarantar koyan halshen Sinanci dake ƙasar.
Nan gaba a yau Wen Jiabao, zai tashi zuwa Afrika ta kudu, inda bayan nhan zai ziyarci Angola da Tanzania