Weltbank Korruption | Siyasa | DW | 31.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Weltbank Korruption

Shugaban bankin duniya Paul Wolfowitz, ya gabatar da sabon tsari na game dabada talafi wa kasahen duniya.

Shugaba Paul Wolfowitz,yayi hakan ne dangane da Irin matsi da ya samu na game da bukatar samun sauyin,na yaki da cin hancin ,wanda ya samu daga gun manyan kasashe da suka nemi a sake duba batun.

Wolfowitz yace ya gana da gwamnatoci,tare ma da kungiyoyin al’umma waje ganin ba a kara wahalar da talakawa ba,matukar ya nemi cigaba da manufar yaki da rashawan kamar yadda ya shirya a da can.

A babban taron bankin na shekara-shekara da ya gudana a watan satumba a Singaore,Wolfowitz ya sami galgadi gun kasashe da dama daga turai da kuma kasashe masu tasowa game da batun sauya ka’idojin da suka shafi batun cin hanci da rashawan gabanin bukatun talakawa.

Kasashe kamar su Birtaniya,Faransa da Jamus kowanen su ya nuna damuwa game da tsauraran matakai kann tsarin taimakon raya kasa da bakin duniyan ke yi.

Wolfowitz ya sami goyon bayan babban sakatarin asusun taimako na Amurka Henry Paulson,wanda ya kwatanta cin hanci da rashawa a matsayin wani salon haraji mafi tsanani da ake sanyawa kan jama’ar kasa.

Wannan shiri na Wolfowitz tun farko,ya hada batun agaji na bankin duniyan da irin kokari na kasashen da za su ci moriya za su yi,wajen samar da gwamnati na gari mai gudanar da ayuka dai dai,da kuma nuna adalci wajen gudanar da aiki.

Amma a nasa jawabin tsohon mukaddashin sakatarin tsaro na majalisar yace za a iya hade wuri guda batun bada agaji ba tare da matsala ba, da kuma aikin kawar da talauci.

Sabon tsarin na yaki da cin haci da rashawa na bankin duniyan za a gabatar da shi gaban taron da zai gudana abirnin Washinton a watan Afrilu,tsakanin Hukumar gudanarwa na bakin duniyan da Asusu bada lamuni na duniya,domin muhawara a kai.

Wanda Eckhard Deutscher,wakilin Jamus na bankin duniya yace daga bisani ne za a zattas da sabon tsarin a kashen shekarar aiki na bankin.

Daga karshe Wolfowitz ya bayyana cewa ,zai dukupa ne wajen aiki tare da gwamnatoci,amma zai fi bada karfi wajen aiki da kungiyoyi masu zaman kansu,kungiyoyin jama’a da kuma manema labarai.

Ya kara da cewa zai kuma yi aiki ne domin ya karfafa tsarin kasashen ba yin watsi da su ba .