Waye ya kirkiro kujerar Lantarki | Amsoshin takardunku | DW | 09.01.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Waye ya kirkiro kujerar Lantarki

Bayani akan kujerar Lantarki wadda ake kashe Mutane da ita

Kujerar Lantarki

Kujerar Lantarki

Jamaa masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na wasikun ma su sauraro,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon, ta fito daga Hannun Malam Yakubu Sulaiman daga Garin Jalingo a Jihar Taraban Tarayyar Najeriya, Malamin yana tambayane game da Mutumin da ya Kera Kujerar Lantarki, wato (Electric Chair) a Turance; Wadda ake amfani da ita wajen kashe mutanen da aka yankewa hukuncin Kisa.

Amsa: Kujerar lantarki wata hanya ce ta kashe mutumin da aka yankewa hukuncin kisa. Kuma wannan hanya ta kisa da kujerar Lantrki amfi amfani da ita a Kasar Amurka. Ko da yake dai a yanzu haka aiwatar da kisa ta wannan hanya yana raguwa.

Binciken da muka yi ya nuna mana cewa, akwai mutane da dama da suke ikirarin cewa sune suka kirkiro wannan fasaha ta kera kujerar lantarki. Amma dai Mutumin da ya kera kujerar lantarki ta farko da aka fara aiwatar da hukuncin kisa da ita shine, Mr. Harold Brown, ko da yake dai shima ya yi ta yin gwaje-gwaje daban a karkashin kulawar Mr. Thomas Edison kafin ya kera kujera ta farko da aka fara kashe Mutum da ita a Kasar Amurka

A shekarar 1888 ne dai, Mr. Brown ya rubata wata wasika zuwa ga mujallar New York Pos, ta Amurka, yana mai basu labarin wani yaro da ya Mutu sakamakon taba wata wayar lantarki da ya yi tsirararta , wadda aka hada ta da wata wayar tangaraho. To dama Kasar Amurka tana neman wata hanyar kisa wadda zaa rinka amfani da ita a maimakon rataye Mutumin da aka yankewa hukuncin kisa, saboda tsananin mahawarar da ake yi akan kisa ta hanyar ratayewa.To sakamakon wannan wasika da Mr. Brown ya rubata, sai Mr. Edison y dauko hayarsa domin ya taimaka yake ra kujerar lantarki.

Kisa na farko dai a Duniya da aka fara aiwatarwa da kujerar lantarki, an yi shi ne a shekarar 1890, kuma kisan ya kasance mai tsanani kwarai-da-gaske, sabanin yadda aka zaci cewar zai zo da sassauci. Kusan har ya nemi ya fi ratayewa azaba.An dai aiwatar da wannan kisa ne akan wani dan fursuna, kuma mai kashe Mutane mai suna William Kemmler.Amma dai sai da aka jona masa lantarkin har sau biyu kafin ya rasu. Sananniyar Jaridar nan ta New York Herald ta bayyana irin yadda wannan kisa ya gudana. Inda masharhanta da dama suka tabbatar da cewa, hanyace ta azaba da wahalarwa kwarai-da-gaske.

A binciken da muka yi, mun gano mutane 26 da aka kashe ta hanyar kujerar lantarki, kuma dukkaninsu yan-kasar Amurka ne. Mutane na baya bayan nan sun hada da; Mr. Earl Conrad Bramblett, Dan Jihar Virginia, wanda aka kashe a shekara ta 2003. Sai Mr. James Neil Tucker, Dan Jihar South Carolina, wanda aka kashe a shekara ta 2004. Sai kuma Mr. Brandon Hedrick shi ma Dan Jihar Virginia wanda aka kashe a shekara ta 2006.

 • Kwanan wata 09.01.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvV3
 • Kwanan wata 09.01.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvV3