1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata ´yar Iraqi ta amsa cewa ta kasa ta da bam a jinkinta a harin birnin Amman

Wata mata ´yar Iraqi ta amsa cewar ta gaza a kokarin ta na ta da wasu bama-bamai da ta daure a jikinta a daya daga cikin hare haren da aka kaiwa wasu otel otel guda 3 a birnin Amman. Miji na ya daura wani bel mai dauke da bama-bamai sannan ya sanya mini daya kuma ya nuna mini yadda zan ta da su, inji Sajida Mubarak Atrous al-Rishawi mai shekaru 35 lokacin da ta bayyana a gidan telebijin din Jordan daure da wani farin dan kwali da bakin hijab da kuma wani abu mai kama da igiyar bam daure da kugun ta. Sajida ta ce bam din ta ya ki yin bindiga to amma mijin ta ya ta da wanda ya daura a jikinsa. Sauran mutane ukun da suka kai harin kunar bakin wake ciki har da mijinta sun mutu. Hare haren da aka kai kan otel otel din a ranar laraba sun halaka mutane 57 sannan kimanin 90 sun samu raunuka.