Wata turereniya a Filipins ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 66 | Labarai | DW | 04.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata turereniya a Filipins ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 66

Akalla mutane 66 suka rigamu gidan gaskiya a wata turereniya da ta auku lokacin da mutane suka yi layin sayen tikitin kallon wani wasan telebijin mai farin jini a wani filin wasa dake Manila babban birnin Filipins. ´Yan sanda da jami´ai a yankin sun ce turereniyar ta auku ne a filin wasa na Ultra lokacin da masu shirya wasannin na farko suka fara rarraba tikiti ga mutane wadanda daga cikin su akwai wadanda suka shafe kwanaki da dama suna kwana a wajen filin wasannin. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce an shiga yamutsi ne lokacin da wani a ciki gungun mutane ya yi ihun ganin bam amma wasu sun ce rashin hankurin mutane ne ya janyo yamutsin. Daukacin wadanda abin ya rutsa da su tsofaffi ne.