Wata sabuwar guguwa ta ratsa kasar Haiti mai fama da matsalolin talauci | Labarai | DW | 25.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata sabuwar guguwa ta ratsa kasar Haiti mai fama da matsalolin talauci

Wata sabuwar mahaukaciyar guguwa da aka yiwa lakabi da Alpha ta halaka mutane 11 sannan ta yi kaca-kaca da gabar tekun tsibirin Haiti. Kamar yadda wadanda suka shaida abin da ya faru suka nunar guguwar hade da ruwan sama kamar da bakin kwarya sun haddasa mummunar barna a wannan kasa dake jerin kasashen duniya mafi talauci. A kuma halin da ake ciki mahaukaciyar guguwar Wilma wadda yanzu haka take gudun kilomita 200 cikin awa daya ta ratsa yankin jihar Florida. Hukumomi a jihar sun ce akalla mutane 6 sun rasu.