Wata sabuwar fafatawa ta ɓarke a ƙasar Somaliya. | Labarai | DW | 25.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata sabuwar fafatawa ta ɓarke a ƙasar Somaliya.

A ƙalla mutane 38 ne rahotanni suka ce sun rasa rayukansu a wata sabuwar fafatawar da ta ɓarke a birnin Mogadishu, babban birnin ƙasar Somaliya. Jami’an kiwon lafiya a birnin, sun tabbatar cewa a ƙalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu, yayin da ’yan bindigan ƙungiyoyi masu hamayya da juna suka yi ta musayar wuta tsakaninsu yau da safen nan. Wani kwamandan rukunin ’yan bindiga na dakarun islama, Ali Mohammed Siyad, ya faɗa wa maneman labarai cewa, ’yan rukuninsa guda 8 ne suka rasa rayukansu a fafatawar.