1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata mummunar girgizar kasa ta auku a tsibirin Java na Indonesia

Akalla mutane 440 sun rigamu gidan gaskiya sannan dubun dubata sun samu raunuka sakamakon wata mummunar girgizar kasa da ta auku a tsibirin Java dake kasar Indonesia. Yanzu haka dai an kai wadanda suka mutu da kuma wadanda suka jikata a asibitoci dabam dabam dake wannan yanki. Jami´ai na fargabar cewa yawan wadanda suka mutu a wannan girgizar kasa da karfin ta ya kai awo 6.2 a ma´aunin Richter ka iya karuwa. Girgizar ta fi karfi ne a wani yanki mai cike da jama´a dake da nisan kilomita 30 kudu da jami´ar Yogyakarta. Yanzu haka dai an rufe filin saukar jiragen saman birnin. Ko da yake har yanzu babu cikakken bayani, amma rahotanni sun tabbatar da cewa gine gine da dama sun rushe yayin da aka samu katsewar wutar lantarki da wayoyin tarho.