Wata mummunar girgizar ƙasa ta auku a tsibirin Sumatra | Labarai | DW | 02.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata mummunar girgizar ƙasa ta auku a tsibirin Sumatra

Wata mummunar girgizar kasa da karfin ta ya kai awo 6.4 a ma´aunin Richter ta auku a kusa da gabar tekun tsibirin Sumatra na kasar Indonesia. Kamar yadda cibiyar nazarin girgizar kasa a birnin Jakarta ta nunar karfin wannan girgiza na wani wuri mai zurfin kilomita 20 a karkashin teku mai tazarar kilomita 160 daga garin Lais. Ya zuwa yanzu babu rahotanni game da rayukan da suka salwanta ko kuma irin barnar da girgizar kasar ta haddasa. A tsakiyar watan satumba mutane akalla 13 sun rigamu gidan gaskiya sakamakon wata girgizar kasa mai karfin awo 8.4 da ta auku a tsibirin na Sumatra.