Wata mujallar sojin Amirka da ake bugawa a birnin Washington, ta yi kira ga shugaba Bush da ya sallami sakataren tsaron ƙasar Donald Rumsfeld. | Labarai | DW | 05.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata mujallar sojin Amirka da ake bugawa a birnin Washington, ta yi kira ga shugaba Bush da ya sallami sakataren tsaron ƙasar Donald Rumsfeld.

Mujallar nan ta Army Times Publications, ta rundunar sojin Amirka, ta buga wani sharhi, inda ta yi kira ga shugaba Bush da ya sallami sakataren tsaron ƙasar Donald Rumsfeld. Mashrahanta dai na ganin wannan kiran, tamkar wani abin ban takaici ne ga fadar White House, musamman saboda zuwansa kwana ɗaya tak kafin zaɓen majalisar datttijan ƙasar da za a yi a ran talata mai zuwa.

Mujallar dai ta ce Rumsfeld ba shi da mutunci kuma a gaban manyan hafsoshin rundunar soji da majalisar dattijai da al’umman ƙasar ma baki ɗaya. Bugu da ƙari kuma, kwarjininsa sai ƙara dusashewa yake ta yi, saboda duk dabarunsa na yaƙi sun ci tura, sa’annan ana nuna shakku ga salon shugabacinsa. A ƙarshe dai mujallar ta ce duk da ɗora laifin koma bayan da dakarun Amirkan ke samu a Iraqi kan sakataren tsaron, su sojojin ne dai ke ta sadaukad da rayukansu a ƙasar.