Wata mota ta yi bindiga a gaban ginin filin jirgin saman Glasgow | Labarai | DW | 30.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata mota ta yi bindiga a gaban ginin filin jirgin saman Glasgow

Kwana guda bayan bankado wani shirin kai harin bam a London a yau wata mota ta yi bindiga a kofar shiga cikin ginin filin jirgin saman birnin Glasgow na Scotland. To sai dai ba´a sani ba ko wani harin ta´addanci aka so kaiwa ko kuma hakan na da alaka da bama-baman da aka dana a cikin motoci jiya a London. Wani da ya shaida abinda da ya faru ya ce motar ta yi bindiga a gaban kofar shiga filin jirgin saman.

“Na ga wata mota samfurin rangerover ko landrover da wasu mutane mutane da suka yi kokarin shiga ginin filin jirgin sama. Gaba daya sai motar ta kama da wuta sai daya daga cikin mutanen ya yi kokarin bude bayan motar, amma sai ta yi bindiga. Hakan ya sa ginin shi ma ya fara cin wuta.”

A halin da ake ciki an soke tashi da saukar jirage a filin jirgin saman na Glasgow.