Wata kungiyar musulmi ta dauki alhakin harin da aka kaiwa New Delhi
October 30, 2005Wata kungiya da ba´a san ta ba da ke kiran kanta Inquilab ko kuma juyin juya hali ta yi ikirarin kai harin bama-baman 3 a birnin New Delhi da ya halaka mutane 61. Kungiyar ta yi ikirarin ne a cikin wayar tarho da ta bugawa ´yan jarida a birnin Srinagar hedkwatar bangaren Indiya na yankin Kashmir. Kakakin kungiyar Ahmed Yar Gaznavi ya fadawa kamfanin yada labarun yanki wato Kashmir News service cewa za´a ci-gaba da kai irin wadannan hare hare har sai Indiya ta janye dakarunta daga Kashmir. Wasu tashoshin telebijin sun ce kungiyar wani bangare ne na ´yan takifen kungiyar Lashkar-e-Taiba mai goyon bayan Pakistan. ´Yan sanda sun ce ko da yake ba su da wani bayani game da wanzuwar wannan kungiya, amma suna gudanar da bincike. A kuma halin da ake ciki an tsaurara matakan tsaro a daidai lokacin da ´yan sanda ke ci-gaba da neman wadanda ke da hannu a harin. Tuni dai gwamnatocin kasashen duniya suka yi Allah wadai da harin da cewa wani aiki ne na ta´addanci, kuma ko ba dade ko ba jima za´a cafke wadanda suka aikata wannan danya.