Wata Kotun soji a Birtaniya ta ji daga bakin shaida cewa manyan hafsoshin sojin Birtaniyan ne suka ba da umarnin gallaza wa fursunonin Iraqi. | Labarai | DW | 17.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata Kotun soji a Birtaniya ta ji daga bakin shaida cewa manyan hafsoshin sojin Birtaniyan ne suka ba da umarnin gallaza wa fursunonin Iraqi.

Wata kotun sojin Birtaniya, da ke binciken ƙararrakin da aka kawo gabanta game da gallazawa wa fursunonin Iraqi da ake zargin dakarun Birtaniyan da aikatawa, ta ji daga bakin wani shaida cewa, manyan hafsoshin rundunar sojin Birtaniyan ne suka ba da umarnin a azabtad da fursunonin har su galabaita, kafin a kai su gun yi musu tambayoyi. Jaridar nan ta The Times ta ruwaito cewa, Manjo Antony Royce, shaidan da ake yi wa tambayoyi a shari’ar da ake yi wa wasu sojoji 7, waɗanda ake zarginsu da gallazawa wa fursunonin Iraqin, ya faɗa wa kotun yadda shugabanninsu a can sama, suka ba su umarnin gallaza wa fursunonin har matuƙa, kafin a yi musu tambayoyin. Shi dai Manjo Royce, ya ce da ya sami wannan umarnin, ya tuntuɓi mai bai wa rundunar sojin shwara a kan batutuwan shari’a, Manjo Russel Clifton, ko yin hakan daidai ne, saboda a nasa ganin gallaza wa fursunonin ya saɓa wa yarjejeniyar Geneva, wadda ta haramta azabtad da fursunonin yaƙi. Amma sai Manjo Cilfton ya ce masa ya aiwatad da umarnin, babu wani abin tantama gare shi.

Amma a ƙarshe, da labarin ya fito a bainar jama’a, sai su manyan suka janye hannunsu, suka ɗora musu duk laifin, inji shaidan.