1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wata kotun Faransa ta yankewa ´yan kishin Islama su 27 hukunci dauri a gidan maza

June 14, 2006
https://p.dw.com/p/Buty

Wata kotu a Faransa ta yankewa wasu mutane sama da 20 hukuncin dauri a kurkuku daga wata shida zuwa shekaru 20. Mutanen wadanda ake zargi masu kishin Islama ne, an same su da laifin yunkurin kai hare hare akan hasumiyar nan ta birnin Paris wato Eifel Turm da kuma wasu wurare masu muhimmanci dake babban birnin na Faransa. An caji mutane 27 da kasancewa ´ya´yan wata kungiya da ake yiwa lakabi da Chehen connection. Galibin shugabannin kungiyar ´yan kasar Aljeriya, wadanda ake zargi da samun horo ko dai a Afghanistan ko kuma a janhuriyar Chechniya wadda ke son ballewa daga tarayyar Rasha. Masu bincike sun bankado wannan makarkashiya ta kaiwa Paris hari lokacin da suke binciken wasu mutane dake tura matasa zuwa filin daga a Chechniya.