Wata Kotu a Spain, na zargin sojojin Amirka guda 3 da kashe wani dan kasar a Iraqi. | Labarai | DW | 20.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata Kotu a Spain, na zargin sojojin Amirka guda 3 da kashe wani dan kasar a Iraqi.

Wata babbar kotu a kasar Spain ta ba da umarnin kame wasu sojojin Amirka guda 3, saboda tuhumar da ake yi musu na kashe wani dan jaridar kasar Spain din a lokacin yakin Iraqi.

Kotun dai na zargin sojojin ne, da bude wa wani Otel a Bagadaza wuta daga tankunan yakin da suke ciki, a cikin watan Ifirilun shekara ta 2003. A wannan lokacin dai, kusan duk maneman labarai daga ketare, na sauka ne a wannan masukin, wato Otel Palestine. Amirka ta ce sojojin ba su da wani laifi, duk da amincewar da hukumar sojinta ta yi, ta cewar dakarunta ne suka bude wa Otel din wuta da tankin yakinsu.

A halin da ake ciki dai, babu tabbas, ko Amirkan za ta amince ta mika wa Spain sojojin.