Wata kotu a Nigeria ta yankewa Tafa Balogun hukuncin dauri na wata shida | Labarai | DW | 22.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata kotu a Nigeria ta yankewa Tafa Balogun hukuncin dauri na wata shida

Wata babbar kotu a Abuja, babban birnin tarayyar Nigeria ta yankewa tsohon sifeto janar din kasar, wato Tafa Balogun hukuncin daurin watanni shida a gidan yari, a hannu daya kuma da biyan tara ta naira dubu dari biyar, kwatankwacin dalar Amurka dubu 3 da 760.

Kotun karkashin mai sha´ria Binta Nyako tace ta yankewa Balogun wannan hukuncin ne bisa samun sa da laifin yin almubazzaranci da makudan kudade da yawan su ya tasamma dalar amurka miliyan 128.

A yayin da kotun take yanke wannan hukunci a karkashin mai shari´a Binta Nyako, kotun tace ta yankewa Balogun wannan hukuncin ne mai sauki a bisa amsa laifuffukan da ake zargin sa da aikatawa cikin sauri ba tare da wahalarwa ba.

Rahotanni dai daga kasar na nuni da cewa Tafa Balogun ya shafe kusan kwanaki 67 a hannu a don haka za a kwashe wadan nan kwanaki ne daga cikin watann shidan da aka yanke masa.

Ya zuwa yanzu dai Balogun, na a matsayin wani babban jami´i a kasar da aka yankewa hukunci dake da nasaba da cin hanci da rashawa a tun lokacin da aka zabi shugaba Obasanjo a shekara ta 1999.