1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wata girgizar kasa ta auku a cikin tekun tsibirin Sumatra a Indonesia

November 19, 2005
https://p.dw.com/p/BvKO

Wata gawurtacciyar girgizar kasa ta karkashin teku ta auku a arewacin tsibirin Sumatra na kasar Indonesiya a yau asabar. To sai dai kawo yanzu ba wani karin bayani game da irin barnar ko kuma salwantar rai da girgizar kasar ta haddasa. Hukumar hasashen yanayi a birnin Jakarta ta ce girgizar kasar wadda karfin ta ya kai awo 6.5 a ma´aunin Richter ta auku ne a karkashin tekun Indiya amma ba ta haddasa ambaliyar igiyar ruwa ba.