1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata ƙazamar fafatawa ta ɓarke a ƙasar Cadi.

A sake wata ƙazamara fafatawa tsakanin dakarun gwamnatin Cadi da ’yan tawayen ƙasar, abin da ke janyo fargabar cewa, rikicin yankin Darfur zai ƙara yaɗuwa zuwa Cadin. Ministan tsaron ƙasar Cadin, Janar Bichara Issa Djadallah, ya ce dakarun gwamnatin sun kara da wani ayarin ’yan tawayen a gabashin ƙasar, inda dubban jama’a ke zaman gudun hijira sakamakon rikicin yankin Darfur. Rahotanni sun ce, an kashe wani babban kwamandan rundunar sojin Cadin, a ɗauki ba daɗin. Tun ran asabar da ta wuce ne dai Cadin ta zargi Sudan da kai harin bamabamai a kan wasu garuruwa 4 da ke kusa da kan iyakarsu a gabashin ƙasar, kusa da yankin Darfur. Tuni dai Sudan ta yi watsi da wannan zargin. Har ila yau dai, ba a sami wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatad da wannan harin ba.