Wasu ′yan Najeriya da ke Libiya sun koma | Labarai | DW | 25.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wasu 'yan Najeriya da ke Libiya sun koma

Fiye da mutun150 ne suka koma kasarsu Najeriya, bayan da suka kasance tsawon watanni a tsare a kasar Lbiya a kokarin da suke na ketarawa zuwa kasashen Turai.

'Yan Najeriya da suka sauka a filin jirgin saman Lagos cikin murna da annashuwa, yayin da wasunsu ke zubar da hawaye sabili da irin bakar wahalar da suka gani a baya, sun ci gaba da rera wakoki suna cewa, "Najeriya kasarmu ta gado, ba za mu kara barin kasarmu Najeriya zuwa wata kasa ba".

Cikin kasa da watanni biyu dai, wannan shi ne karo na hudu da jirgin yake dauko 'yan kasar ta Najeriya daga Libiya, inda daga farkon wannan shekara ta 2017 zuwa yanzu akalla mutane 660 suka samu shiga cikin wannan tsari na mayar da wadanda suke bukata zuwa kasashensu da kungiyar kula da 'yan gudun hijira ta kasa da kasa OIM ta shirya tare da hadin gwiwar hukumomin Najeriya.

Gabaki daya dai a shekara ta 2016, an samu dawo da mutane 867 ya zuwa gida Najeriya daga kasar ta Libiya.