1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu ’yan bindiga, sun yi garkuwa da wani jami’in diplomasiyyan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a Iraqi.

May 17, 2006
https://p.dw.com/p/Buy0

Rahotannin da ke iso mana daga birnin Bagadazan Iraqi, sun ce wasu ’yan bindigan da ba a san asalinsu ba tukuna, sun yi garkuwa da wani jami’in diplomasiyyan ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, bayan sun harbe ɗaya daga cikin jami’an tsaron da ke kare lafiyarsa. Jami’an gwamnatin Iraqin sun ce wannan lamarin ya auku ne jiya daddare, a misalin ƙarfe 10, a unguwar nan ta Mansour, a birnin Bagadazan.

A cikin watan Yulin bara, ’yan ƙungiyar Al-Qaeda sun yi garkuwa da wasu jami’an diplomasiyya guda biyu daga Aljeriya da kuma ɗaya daga Masar, waɗanda kuma duk suka halaka su, a fafutukar da suke yi ta hana ƙasashen Larabawa da na musulmi ƙarfafa hulɗoɗin dangantaka tsakaninsu da gwamnatin Iraqin da Amirka ke ɗuare wa gindi.