Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 29 a birnin Bagadaza. | Labarai | DW | 31.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 29 a birnin Bagadaza.

Rahotannin da suka iso mana ɗazu-ɗazun nan daga Iraqi, na nuna cewa, wasu ’yan bindigan da ba a san asalinsu ba tukuna, sun kutsa cikin wani shagon sayad da tarho na salula da kuma ofishin hulɗodin cinikayya tsakkanin Amirka da Iraqi a birnin Bagadaza, inda suka yi garkuwa da mutane 26. Kafin wannan ɗaukin, sai da ’yan bindigan suka yi garkuwa da wani riƙaƙƙen ɗan kasuwa da ’ya’yansa maza biyu yau da safen nan. Su dai ’yan bindigan suna sanye ne da rigunan sojin Iraqi. Sun iso tsakiyar birnin Bagadazan ne cikin motocin jeep-jeep guda 15, a unguwar Karrada mai yawan kantuna. Wani kakakin ’yan sandan birnin Bagadazan, Laftanan Tahir Mahmood, ya ce kai tsaye bayan isowarsu ne ’yan bindigan suka rarrabu, wani rukuni ya cafko ma’aikatan ofishin salulan su 15, ya yi awon gaba da su, sa’annan ɗaya rukunin kuma ya sace mutane 11 daga ofshin hulɗar kasuwancin Amirka da Iraqi. Duk ɗaukin dai bai wuce minti 10 ba, inji Laftanan Mahmood, kuma ’yan bindigan sun tsere cikin motocinsu tare da mutanen da suka yi garkuwa da su, kafin jami’an tsaro su iso a gun.

Har ila yau dai a birnin Bagadazan, wasu rahotanni kuma sun ce, ’yan bindiga sun harbe wani babban jami’in ƙungiyar leƙen asirin Iraqin, Birgediya Fakhri Jamil har lahira, a cikin motarsa yau da safen nan, a unguwar Yarmuk da ke yammacin Bagadaza. Taɓarɓarewar halin tsaro a birnin Bagadazan a kwanakin bayan nan dai, ya sa ana ta kira ga sake ministan harkokin cikin gida na ƙasar.