Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikatan haƙo man fetur na kamfanin Shell a tarayyar Najeriya. | Labarai | DW | 15.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikatan haƙo man fetur na kamfanin Shell a tarayyar Najeriya.

Rahotannin da muka samu ɗazu-ɗazun nan daga tarayyar Najeriya, sun ce wasu ’yan bindiga da suka kai hari kan wata kafar haƙo man fetur ta kamfanin Shell a jihar Bayelsa jiya daddare, sun tsere daga kafar, tare da ma’aikatan kamfanin uku da suke garkuwa da su. Wani kakakin kamfanin Shell ɗin, ya faɗa wa maneman labarai cewa, duk waɗanda aka yi garkuwa da sun, ’yan Najeriya ne. Wannan dai shi ne karo na biyu da aka kai hari kan wata kafar haƙo man fetur a jihar ta Bayelsa a cikin kwanaki 8, bayan da wasu ’yan ta kife suka yunƙuri ragargaza wata tashar jigilar mai da bamabamai, da kuma yin garkuwa da ma’aikatan haƙo man fetur daga ƙetare a makon da ya gabata.