1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu ' yan bindiga sun kashe Babakura Fugu

September 17, 2011

Mtumin da ya gana da tsohon shugaban ƙasar Najeriya wato Olusegun Obasanjo da sunnan iyalen marigayi Muhammed Yusuf shugaban ƙungiyar boko haram shi ne wasu mutane da ba a tantance ba suka bindige

https://p.dw.com/p/12bMD
Taswirar'Najeriya

Wasu ‘yan bindiga da ba'a tantance ko su waye ba, sun hallaka Babakura Fugu dan marigayi Baba Fugu Muhammad surukin Muhammad Yusuf Shugaban Kungiyar Boko Haram.

Shi dai Babakura dan shekaru 32 shine ya karbi tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a yayin da ya ziyaci iyalan marigayi Muhammad Yusuf a wani mataki da ake gani na neman warware rikicin da Birnin Maiduguri da wasu sassan Najeriya ke fama da shi. Maharan waɗanda ke cikin wata mota kirar Golf sun bude masa wuta a kofar gida yayinda yake shirin yin alwala don yin sallah.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi