wasu yan bindiga a Japan sun jikkata wani basarake a kasar | Labarai | DW | 17.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

wasu yan bindiga a Japan sun jikkata wani basarake a kasar

Wasu ‚yan bindiga sun jiwa magajin garin Nagasaki dake kasar Japan raunuka, a lokacin da suka kai masa hari, a yayin da yake gudanar da yakin neman zabe, kusa da wata tashar jiragen kasa. Magajin garin mai shekaru 61 da haifuwa, Mai suna Itno Ito, na neman sake darewa kujerar shugabancin jahar, karo na hudu a lokacin da abin ya same shi. Majiyan ‚yan sanda dai tace babu wani takamaimiyar labari akan sanadiyar harin ba.