Wasu Sojoji a Nijar na adawa da kafa cibiyar sojojin ketare a kasar | Siyasa | DW | 10.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sakamakon rahoton kungiyar GRIP kan Nijar

Wasu Sojoji a Nijar na adawa da kafa cibiyar sojojin ketare a kasar

Sakamakon wani bincike da kungiyar GRIP ta gudanar, ya nunar cewa wasu sojojin kasar Nijar da fararan hulla da dama na adawarsu ga zaman sojojin kasashen ketare a kasar.

Sojoji 850 ne dai kasar Jamus ke shirin girkewa a kasar ta Nijar domin gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro musamman na dafa wa dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya masu yaki da ayyukan ta'addanci a yankin Sahel. Sai dai sakamakon wani rahoton bincike da kungiyar GRIP wato "Groupe de recherche et d'information sur la paix et la securite"  da ke bincike kan harakokin tsaro da zaman lafiya ta wallafa a ranar bakwai ga wannan wata na Nuwamba, ya nunar cewa sojojin na Nijar da dama na adawa da zaman rundunonin sojojin kasashen Turai da Amirka a cikin kasar. Geroges Berghezan shine ya jagoranci binciken na kungiyar ta GRIP ya ce akasarin sojojin da aka tambaya a cikin rukuni daban-daban na rundinonin sojojin kasar, sun ce ba su ga amfanin zaman wadannan sojoji na Faransa da Amirka a cikin kasar ta Nijar ba:

"Ya ce hujja ta farko da suke bayar wa, suna ganin tamkar keta haddin 'yancin kasa ne , sannan kuma suna ganin zaman sojojin wadan nan kasashe a cikin kasar ta Nijar ba shi da wani amfani ga kasar, domin babu wani taimako da hakan ke kawo wa sojojin na Nijar a cikin ayyukansu na yau da kullm. ya ce sun bada musalai daban-daban na tabbatar da haka. Wannan ta sanya da dama daga cikinsu suke nuna adawa ko kuma kosawarsu da zaman sojojin na waje"

 

A shekara ta 2010 ne bayan da kungiyar AQMI ta Al-Qaida a yankin Sahel, ta sace wasu ma'aikatan kamfanin Areva na Faransa mai hakar karfen Uranium a garin Arlit a arewacin kasar ta Nijar, sojojin Faransar suka soma girkuwa a kasar, sannan kuma sun kara samun gindin zama a lokacin da aka kafa rundunar tsaro ta sojojin na Faransa ta Barkhane a shekara ta 2014 domin yakar 'yan ta'adda a yankin Sahel. Wasu daga cikin sojojin na Nijar da aka tambaya sun ce Faransa ta girke sojojin ta ne kawai don ta kare muradun ta, sojojin na Faransar na hada baki da kungiyoyin 'yan ta'adda domin tayar da zaune tsaye a cikin kasar ta Nijar a cewar wasu sojojin da aka tambaya. Sai dai adawa da girke sojojin kasashen ketare a kasar ta Nijar ba ta tsaya ga sojoji ba kawai a cewar Musa Aksar wani dan jarida mai sharhi kan harakokin tsaro a kasar ta Nijar:

" Ya ce babu wata shawara da aka nema ga mafi yawancin 'yan kasa wajen girke wadannan sojoji a cikin kasa, kuma wannan ce ta haifar da cecekuce . Kamata ya yi a ce gwamnati ya nemi izinin majalisar dokoki kafin ba dada izinin girkuwar wadannan rundunoni wadanda a ganina na da muhimmanci wajen yaki da ta'addanci a yankin na Sahel."

 

Rahoton kungiyar ta GRIPP, ya nunar da cewa da farko dai adadin sojojin Faransa ya kai kimanin 350 yayin da na Amirka ya kai 200 a yankin na Sahel, sai dai duk da adawar da ake nunawa a game da hakan, amma kuma  adadinsu ya karu bayan da harkokin tsaron suka kara tabatbarewa a sakamakon ayyukan kungiyar Boko Haram.