Wasu Jami′oin Jamus za su rinka koyar da darussan addinin Musulunci | Labarai | DW | 14.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wasu Jami'oin Jamus za su rinka koyar da darussan addinin Musulunci

Jamus ta shirya fara koyar da darussan addinin Musulunci a wasu jami'oin ta daga shekara ta 2011

default

Schavan da Merkel

Daliban kasar Jamus da ke son mayar da hankalin su ga koyon darussan addinin Musulunci za su sami horo a wasu jami'oin kasar guda ukku, farawa daga shekara mai zuwa - idan Allah ya kaimu. Ministan kula da harkokin Ilimi a Jamus Annete Schavan ta fadi a wannan Alhamis cewa Makarantun jami'oi a biranen Thübingen, da Münster da kuma Osnabrück za su bude sabbin sassan koyar da darussan addinin musulunci, inda kuma hukumomi suka warewa shirin kudin daya kai na Euro miliyan hudu a cikin tsukin shekaru biyar masu zuwa.

Daliban na Jamus za su sami horo ne domin zama Limamai da kuma malaman koyar da sha'anin addinin Musulunci. Ministar ta ce hukumomin Jamus suna bada muhimmanci ga sabon shirin:

"Kamata yayi limamai su zama tamkar gada a maimakon su zama masu hana ruwa gudu wajen kyautata cude-ni-in-cude-ka. A saboda haka a ganina ya zama abu mai muhimmanci a bai wa limaman damar neman karin ilimi a nan Jamus, ta yadda zasu fahimci zamantakewar jama'a a kasar da suke da niyyar tafiyar da aikinsu a cikinta."

Ministar ta ce dama jami'oin sun shahara wajen koyar da darussan addinin Kiristanci a baya, inda a yanzu kuma za su bude sassan koyar da addinin Musulunci a shekarar karatu ta 2011. Ministar Ilimin ta Jamus Annete Schavan ta yi wannan sanarwar ce a dai dai lokacin da ake ci gaba da tafka muhawara game da batun sajewar 'yan ketare mazauna Jamus da irin al'adu da dabi'un Jamusawa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijani Lawal