1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu daga cikin shugabannin duniya da su ka rasu akan mulki.

June 17, 2010

Tarihi da takaitacciyar rayuwar wasu daga cikin shugabannin duniya da suka rasu a karagar mulki.

https://p.dw.com/p/Nu0n
Tshohon shugaban Amirka John F. KennedyHoto: picture-alliance/dpa

Binciken da muka gudanar ya nuna cewar akwai shugabanin ƙasashen duniya da dama da suka rasu suna kan karagar mulki kama daga Nahiyar Amirka zuwa Turai da Asia da kuma Afrika ko kuma gabas ta tsakiya. Sai dai wannan bai haɗa da shugabanni irin na mulki mulukiya ko Sarakuna ba.

Idan muka fara daga ƙasar Amirka shugabanni 8 ne kawai daga cikin 44 suka rasu akan karagar mulki. Na farko dai shine William Henry Harrison wanda ya rasu a ranar 4 ga watan afirilun 1841, sai Zachary Taylor wanda ya rasu a ranar 9 ga julin 1850, sai kuma Abraham Lincoln wanda ya rasu a ranar 15 ga watan Afirilun 1865. AKwai kuma Abraham Garfield wanda ya rasu a ranar 19 ga watan Satumban 1881 sai William McKinley Jnr. wanda ya rasu a ranar 14 ga Satumban 190, sai Warren Gamaniel Harding wanda ya rasu a ranar 2 ga watan Augustan 1923, haka kuma akwai Franklin Delano Roosevelt wanda shi kuma ya rasu ne a ranar 12 ga Afirilun 1923 sai John F. Kennedy wanda aka kashe a ranar 22 Nuwanban 1963.

Idan kuma muka koma Birtaniya akwai Firaministoci 7 da suka rasu akan mulki na farko dai shine Spencer Comton wanda ya rasu a ranar 2 ga julin 1743 da Henry Pelham 6 ga Maris ta 1754, sai kuma Charles Watson-Wentworth wanda ya rasu a ranar 1 ga watan Julin 1782, akwai kuma William Pitt wanda ya rasu a ranar 23 Janairun 1806. Shi kuwa Spencer Perceval ya rasu ne a ranar 11 ga mayun 1812. Sauran Firaministocin da suka rasun sun haɗa da George Canning 8 ga watan Augustan 1827, sai Henry Temple a ranar 18 ga watan Oktoban 1827.

Präsident Nigeria Umaru Yar'Adua
Marigayi shugaban Nijeriya Umaru Musa Yar'AduaHoto: picture alliance/dpa

Idan kuma muka koma nahiyar mu ta Afirka akwai Gammal Abdul Nasser da Anwar Saddat, sai kuma William Tubman a Liberiya da Firaminista Patrice Lumumba na Congo da Sylvio Olympio na Togo da kuma Felix Houphoet na Cote d'Ivoire. Akwai kuma Omar Bango na Gabon da Kuma Levy Mwanawasa na Zambiya da Samuel Doe na Liberiya. A Nijer akwai Ba'are Mainasara.

Idan muka gangaro Najeriya kuwa akwai Abubakar Tafawa Balewa wanda ya rasu a ranar 15 ga janirun 1966, sai Manjo Janar Johnson Thomas Aguiyi-Ironsi a ranar 29 ga watan Julin 1966. Akwai kuma Janar Murtala Ramat Muhammed a ranar 13 ga Janairun 1976. Sai kuma janar Sani Abacha 8 ga watan junin 1998. Sai kuma Umaru Musa Yar'adua wanda ya rasu a ranar 6 ga mayun 2010.

Mawallafi : Babangida Jibril

Edita : Ahmed Tijani Lawal