Wasu bakin haure na Afrika sun sake kokarin ketarawa Turai | Siyasa | DW | 05.10.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Wasu bakin haure na Afrika sun sake kokarin ketarawa Turai

Kimanin bain haure 100 ne suka samu kutsawa cikin kasar Spaniya daga kasar Maroko

Bakin haure a Melilla

Bakin haure a Melilla

Wannan shine yunkuri na baya cikin kwanakin nan da yan kasar ta Moroko sukeyi na ketarawa zuwa garin Melilla dake nahiyar Turai daga bakin iyaka kasar da kasar Spaniya.

A makon daya gabata wasu mutane bakin haure biyar sun rasa rayukansu a wani yunkurin irin wannan inda suke anfani da karfin yawansu domin shiga nahiyar ta turai.

Har yanzu kuma baa san kowa ya harbi wadannan mutane ba.

Matasa yan Afrika kusan 60 da rigunansu da kuma hannayensu sun kekkece,suna jira bakin ofishin yan sanda suna fatar samun yin rajista,domin kare sake maida su Maroko.

Wasu da dama kuma da suka samu rauni an tafi su asibitin sojoji na birnin Melilla.

Wannan shine karo na biyu cikin wannan mako da bakin haure na Afrika suke kokarin kutsawa nahiyar ta turai a wani sabon salo da suka kirkiro na anfani da karfi wajen shiga nahiyar,wani abu da yanzu yake matukar damun mahukuntan kasar Spaniya inda suka baiwa wani kanfani kwangilar gina sabon katangan karfe a yankunan Melilla da Ceuta dake bakin iyaka.

A halin yanzu dai Kungiyat Taraiyar Turai tace zata tura kwararru zuwa kasar Moroko domin taimaka nemo bakin zaren warware wannan matsala ta bakin haure.

A jiya talata ne komishinan tsaro na Kungiyar Taraiyar Turai,Franco Frattini,yace tawagar ta Kungiyar ta Turai zata duba halin da ake ciki a bakin iyakokin kasar Maroko da haniyar Turai,musamman a yankunan kudancin tekun Mediteranean.

Yawan mutane dake kokarin ketara iyakar sai karuwa sukeyi cikin yan watannin nana inda jamaa da dama daga kasashen Afrika dabam dabam da suke gujewa talauci suke bi ta kasar Moroko domin su ketara zuwa turai a kokarinsu na samun ingantacciyar rayuwa.

Bakin haure na Afrika guda 7 suka rasa rayukansu cikin kwanaki na a kokarinsu na shiga turai din, biyar daga cikinsu a ranar alhamis da ta gabata a garin Ceuta.

Kasar Spaniya dai a halin yanzu tace zata kafa kemarori a bakin iyakikinta ,yayinda kasar Maroko kuma tace zata kara yawan yan sandanta a cikin dazuzzuka dake bakin iyaka kasashen biyu.

A jiya talata yan sandan Maroko sun tsare mutane 136 dake kokarin ficewa a garin Nador da ke kusa da garin Melilla.

Daruruwan bakin haure da suka kwashe watanni ko kuma shekaru suna tafiya cikin saharar Afrika suna nan zaune cikin dazukan Maroko masu tazarar kilomita goma daga bakin iyaka turai, suna masu jiran samun damar ketarawa zuwa turai.

Mutanen da aka ce yawancinsu daga kasashen Afrika ta yamma suke,su kan gina kuranga da suke anfani da su wajen tsallaka shingayen karfe dake bakin iyakar inda yan sandan Maroko da na Spaniya suke gadi.

Ita dai kasar Spaniya bata kulla wata yarjejeniyar maiyarda bakin haure zuwa kasashensu ba tsakaninta da mafi yawan kasashen Afrika,saboda haka ba damar ta mayar da bakin hauren muddin sun samu shiga kasar.

 • Kwanan wata 05.10.2005
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvZB
 • Kwanan wata 05.10.2005
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvZB