Wassanin ranar farko na gasar cin koffin ƙwallon kafa | Siyasa | DW | 10.06.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Wassanin ranar farko na gasar cin koffin ƙwallon kafa

A ranar farko ta wassanin gasar cin kofin ƙwallo ta dunia, Jamus ta ci Costa Rica 4 da 2, a yayan da Ecuado ta ci Polland 2 da 0

default

Jiya ne a ka fara gasar cin kofin ƙwallan ƙafa ta dunia a nan ƙasar jamus.

Karon farko ya haɗa ƙungiyoyi 4 na group A, inda Jamus ta buɗe fage da Costa Rica, a birnin Munich, sannan Poland, ta kara da Ecuado a Gelsenkirchen.

Masu sauraro kamar yada ƙila ku ka riga kuka sani, Jamus mai masaukin baƙi ta lashe takwarar ta, Costa Rica, da ci 4 da 2.

Masu kulla da harakokin ƙwallo na shaidar da cewa, lalle ƙungiyar ƙwallan Mannchafts ta yi abun a zo a gani, to saidai duk da haka, akwai yan ƙananan kura-kurai, a ɓangaren masu kulla da kariyar gida wato Defense, inda ta nan ne yan Costa Rica su ka samu sukunnin saka ƙwallo so 2 .

Duk da cewar an ci su, yan wassan Costa Rica ba kanwar lasa ne ba.

Wannan shine karo na farko, a tarihin wasan cin koffin ƙwallo ta dunia ,inda tun tashin farko aka saka ƙwalaye har 6 a raga.

A daren jiya, jamusawa sun kwan da farin ciki.

A duk tsawan daren, matasa ma´abuta ƙwallo, sun sheƙe ayar su, tare da kaɗakaɗe da rayeraye da shaye shaye.

Sun na masu jinjina dantse, ga mai koyar da yan wassa Jürgen Klinsmann.

Yanzu sai juya ga wassa na 2, da ya haɗa Polland da Ecuado a filin ƙwallan AufSchalke Arena na Gelsenkirchen.

Gaban yan kallo kimanin dubu 50 ne,yan Ecuado su ka ba maraɗa kunya, inda su ka yi kaca -kaca da Polland, ci 2 da nema, bayan da Carlos Tenorio da Agustino Delgado su ka yaudari mai tsaran gidan Poland.

Kamin wannan wassa, da dama daga masu sharhi kann harakokin ƙwallo sun zaci Polland zata lashe Ecuado, to saidai kamar yada hausawa kance, ba asan ma ci tuwo ba sai ta ƙare, kuma cemma dai poland, duk da cewa ta fara shiga gasar cin kofin ƙwallo tun shekara ta 1938, ba ta taɓa taka wata rawar a zo agani ba.

A nata ɓangare ƙasar Ecuado, ta fara shiga gasar ƙwallo ta dunia, a karon ƙarshe na shekara ta 2002.

A halin yanzu, abun da ya rage wa ƙasar polland shine na yin iya ƙoƙarin ta, a wassan na 2, da zai haɗa ta da Jamus, ranar 14 ga wata, inda kuma a nan ma ba ta barƙata komai ba , to bisa dukan alamu,, za ta kasance ƙungiyar ƙwallo ta farko da za´a fitar daga jerin masu nemnan kopi a wannan karo.

A yanzu hankulla sun kakarkata, ga wassanin da za ayi yau, a ƙarhe 2 agogon Nigeria da Niger a Francfort, tsakanin Engla da Paraguy, sai kuma wassa na 2 a Dortmund, tsakanin Trinidade da Tobago, da Sudeen, sannan ɗaya daga wakilan Afrika, wato Cote d´Ivoire zata kara a birnin Hamurg da Argentina bakin ƙarfe 6 agogon Nigeria da Niger.

 • Kwanan wata 10.06.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btzm
 • Kwanan wata 10.06.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btzm