Washington ta yi kira ga kasashen duniya da su yi wai taro game da Somalia | Labarai | DW | 10.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Washington ta yi kira ga kasashen duniya da su yi wai taro game da Somalia

Amirka ta yi kira da a gudanar da wani taron kasashe duniya game da halin da ake ciki a Somalia. Kakakin ma´aikatar harkokin wajen Amirka Sean McCormack ya ce Amirka na iya shirya taron farko na sassan dake tuntubar juna game da Somalia a cikin mako zuwa a birnin New York. Hakan dai ya zo ne kwanaki kadan bayan da sojojin sa kai na Islama suka kwace Mogadishu babban birnin Somalia, bayan sun fatattaki kawancen madugan yaki da aka yi imani suna samun kudin tafiyar da harkokin su daga gwamnatin birnin Washington. A kuma halin da ake ciki kungiyoyin da basa ga maciji na hada kawunansu a garin Jowhar mai tazarar kilomita 90 arewa da Mogadishu. Hakan dai ya tilastawa daruruwa mazauna garin tserewa.