1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasannin kwallon kafa na matasa a Berlin

June 29, 2006

Ofisoshin jakadancin Jamus a Nejeriya da ghana sun hana wa wasu kungiyoyin kwallon kafa na matasa guda biyu visar halartar wasannin da za a yi a Berlin daga 2 zuwa 8 ga wata mai kamawa

https://p.dw.com/p/BtzW

Wasannin na kwallon kafa na matasa akan tituna, wanda wannan shi ne karo na farko da aka shirya gudanar da shi daga biyu zuwa takwas ga watan yuli a birnin Berlin, domin kasancewa wani gagarumin bikin da zai tafi kafada-da-kafada da gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya dake gudana yanzu haka a nan Jamus. Da farko dai an shirya kungiyoyi 24 ne zasu halarci wasannin na kwallon kafa na matasa, wadanda suka hada da ‘ya’yan marasa galihu daga kasashe masu tasowa kuma hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ce ke daukar nauyinsa. Amma ga yadda al’amura ke tafiya yanzu haka, bisa ga dukkan alamu kungiyar “Search and Groom” ta Lagos da “Play Succer” daga Accra ba zasu samu ikon shiga a dama da su ba. Domin kuwa ofisoshin jakadancin Jamus a Nijeriya da Ghana sun ki su ba wa ‘yan wasan kungiyoyin biyu visa. Rahotanni na jaridu sun ce jami’an ofisoshin jakadancin Jamus a kasashen biyu sun bayyana shakkunsu a game da cewar ‘yan wasan na da niyyar komawa gida bayan kawo karshen wasannin. Bugu da kari kuma wasu daga cikin bayanan da aka bayar na neman visar kage ne ba kanshin gaskiya tattare da su. Da yawa daga jami’an wasa da wakilan majalisar dokokin Jamus sun yi kakkausan suka akan take-taken jami’an na ofisoshin jakadancin kasar a Nijeriya da Ghana. Hans-Christian Stroebele wakilin jam’iyyar The Greens a majalisar dokoki ta Bundestag ya gabatar da maganar a zaman tattaunawar da majalisar tayi a jiya laraba. Ya kuma yi godo ga ministocin cikin gida da na ketare da su tsoma baki domin jami’an diplomasiyyar su canza salon tunaninsu game da lamarin. Ya ce a ganinsa duk wani dan Ghana ko Nijeriya akan yi masa kazafi ba tare da bincike da tantance gaskiya ba. Irin wannan take-take babban illa ne ga ita kanta gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da ake gudanarwa yanzu haka a Jamus, wadda kasar tayi alkawarin nuna karimci ga dukkan bakin da zasu shigo cikinta tsawon wannan gasa. A lokacin da yake karin bayani Gerhard Buchholz daga wata kafar kasuwanci dake birnin Berlin cewa yayi:

O-Ton

A halin yanzu haka Jamus na cikin wani kyakkyawan yanayi ne na kawance da dukkan mahalarta gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a kasar. Lamarin da ba a taba ganin irin shigensa ba a cikin tarihin kasar. A sakamakon haka shawarar da ofisoshin jakadancin suka tsayar na kin ba wa kungiyoyin nan biyu visa domin halartar wasannin na matasa ko kadan bata dace da yanayin da ake ciki ba. Bugu da kari kuma karamar hukumar Berlin na da cikakkiyar masaniya a game da yadda take tinkarar matsalolin manema mafakar siyasa, a saboda haka ba zata shiga kaka-nika-yi ba in har an fuskanci irin wannan matsala. Amma hana wa kungiyoyin biyu shiga wasannin gaba daya ba abu ne da ya dace ba.”