1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasannin kwallon kafa daga sassa

March 8, 2017

Shahararrun yan wasan kwallon kafa daga nahiyar Africa, na barin manya manyan klub da suke bugawa a Turai zuwa wasu klub-klub a nahiyar Asia musamman ma kasar SIN ko China.

https://p.dw.com/p/2YpS7
Deutschland Borussia Moenchengladbach v FC Schalke 04 - Jubel
Hoto: Getty Images/Bongarts/M. Hitij

A wasannin Bundesliga na karshen mako da aka kara kungiyar kwallon kafa ta Werder Bremen ta doke Darmstadt da ci 2 da nema. Kana Brussia Dormund ta raga-raga da Leverkussen da ci 6 da 2. Haka ita ma Hoffenheim ta ragargaza Ingolstadt da ci 5 da 2. Ana ta bangaren Mönchengladbach da doke Shalke da ci 4 da 2. Yayin da Bayern Munic ta bi FC Kolon har gida ta doke ta da ci 3 da nema.

Yanzu haka a jerin teburin na Bundesliga na Jamus kungiyar kwallaon kafa ta Bayern Munich ke ci gaba da jagoranci da maki 56, yayin da Leipzig ke mara mata baya da maki 49. Brussia Dortmund tana matsayi na uku da maki 43. Ita kuma Hoffenheim tana mataki na hudu da maki 41, sannan Hertha Berlin ta kasance a matsayi na biyar da maki 37.

Hull City vs. Liverpool - Premier League
Premier League: Hull City da LiverpoolHoto: Getty Images/G. Copley

A wasannin La Liga da aka kara a Spain a karshe mako a can ma an yi ruwan kwallaye, inda kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta doke Celta da ci biyar da nema. Kana Real Madrid ta bankare Eibar da ci 4 da 1. Ana ta bangaren Atlético Madrid ta doke Valencia da ci 3 da nema. Sannan Villarreal ta doke Espanyol da ci 2 da banza. Yayin da Las Palmas ta doke Osasuna da cio 5 da 2.

Har yanzu kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ke kan gaba a jerin kungiyoyin La Liga na Spain da maki 60, yayin da Real Madrid ke mara mata baya daf-da-daf da maki 59, inda Sevilla ke matsayi na uku da maki 55. Kungiyar Atlético Madrid ke matsayi na hudu da maki 49 kana Real Sociedad wadda take ta biyar tana ksance da maki 48.

Deutschland Eintracht Frankfurt - SC Freiburg
Bundesliga: Karawar 'yan wasan Frankfurt da Freiburg Hoto: picture alliance/dpa/T. Wagner

A wasannin Premier da aka kara a Ingila kungiyar Crystal Palace ta doke West Brom da ci 2 da nema, yayin da Leicester City da doke Hull da ci 3 da 1. Tottenham ta doke Everton da ci 3 da 2. Liverpool ta doke Arsenal da ci 3 da1.

Kungiyar Chelsea ke jagoranci taburin na Premier da maki 63, mai mara mata baya Tottenham tana da maki 56. Manchester City a matsayi na uku da maki 55, kana Liverpool ta kasance a matsayi na hudu da maki 52, inda Arsenal mai maki 50 ke matsayi na biyar. Manchester United tana matsayi na shida da maki 49.

Shahararrun yan wasan kwallon kafa daga nahiyar Africa, na barin manya manyan klub da suke

bugawa a Turai zuwa wasu klub-klub a nahiyar Asia musamman ma kasar SIN ko China. Na baya bayan nan su ne wasu fitattatun yan wasan Super Eagles na Nigeria da suka fice daga Turai suka rattaba hannu a kwantiragin yin wasa  a wasu klub na China.