1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bundesliga Radio kai-tsaye

Mohammad Nasiru Awal GAT
August 26, 2016

A daidai lokacin da ake shiga kakar wasannin kwallon kafar kasar Jamus ta Bundesliga karo na 57, ma'abota tashar rediyon DW na iya sauraron wasannin kai-tsaye ta akwatunan rediyonsu ko shafin Facebook na DW Hausa.

https://p.dw.com/p/1JpzY
DW Bundesliga Radio Live (Key Visual hausa)

Shirye-shiryen DW Hausa kai tsaye (da Bundesliga a ran Asabar)

Tun daga ranar 27 ga watan Augustan shekara ta 2016 muka fara gabatar da wasannin Bundesliga kai-tsaye ta harsunan Hausa da Suwahili, sannan daga bisani sassan harsunan Faransanci da na al'ummar Portugal suka shiga sahu. A kakar wasanni ta 2019/20 Sashen Ingilishi ya shiga jerin masu kawo muku wannan sharhi na gasar Bundesliga.

Shekarar ta 2019 ta kasance kakar wasanni ta hudu da muke gabatar da bayanai kan Bundesliga. A cewar tsohon abokin aikinmu da ke zama kwararren mai gabatar da sharhi kan harkokin wasannin motsa jiki Umaru Aliyu "wannan tamkar mafarki ne da ya zama zahiri."

 

Gasar wasannin Bundesliga kai-tsaye

Kai tsaye kamar yadda muka saba, ma'aikatanmu ke gabatar muku da sharhin wasu daga cikin wasannin da suka fi kayatarwa tare da hadin kan kwararru a fannin wasannin kwallon kafa na tashar DW.

Ma'abota wasan Bundesligar Jamus a Kano Najeriya. Su kan shirya gasar kwallon kafa albarkacin Bundesliga
Ma'abota wasan Bundesligar Jamus a Kano Najeriya. Su kan shirya gasar kwallon kafa albarkacin BundesligaHoto: DW/M. Mohammed

A cewar shugaban Sashen Afirka na DW Claus Stäcker "Afirka nahiya ce da al'ummarta ke kaunar wasannin kwallon kafa. Kuma masoya kwallon kafar sun san sunayen kusan kowa da ke buga kwallo a tawagar kwallon kafar Jamus da ta sha zama zakara a harkokin wasanni a duniya."

Ma'abota wasannin Bundesliga da dama a nahiyar Afirka ke ba da gudunmawa wajen tallata gasar ta Bundesliga a kowace shekara inda alal misali a birnin Kadunan Najeriya Mohamed Mohamed na tashar Freedom Radio Kaduna, ke shirya gasar Bundesliga a tsakanin kungiyoyin birnin na Kaduna tare da rarraba masu kyaututtuka na Jersey na kungiyoyi dabam-dabam da ke bugawa a rukunin Bundesliga babba irin su Bayern Munich da Dortmund.

 

Shirye-shiryen DW Hausa kai tsaye (da Bundesliga a ran Asabar)

Wasannin Bundesliga a ranaikun Asabar

Za ku iya sauraron shirin na wasannin Bundesligar kai-tsaye da misalin karfe biyu da minti 25 agogon Najeriya, Nijar Kamaru da Chadi, wato karfe daya da minti 25 agogon GMT da Ghana, ta hanyar gajeren zango kan mitoci 19 kilohaz 15195 kilohaz 15350.

Za ku iya sauraronmu kai tsaye ta shafinmu na intanet da na Facebook na DW Hausa lokacin da ake wasan ko kuma a tashoshi abokanan huldar DW da ke a yankunanku a wadannan kasashe:

Najeriya:

BRC -  Bauchi

Caliphate - FM Sokoto

Dandal Kura - Maiduguri

Freedom Radio - Kano, Dutse, Kaduna

Liberty FM - Kaduna, Abuja

Progress Radio - Gombe

Radio Gotel - Yola

Rima FM 97.1 - Sokoto

Platinum FM - Keffi

Prestige FM - Minna

Unity FM - Jos

 

Nijar:

Alternative - Diffa

Anfani - Niamey, Konni, Maradi, Diffa, Zinder

Dallol - Balleyara, Dogondoutchi, Matankari, Tibiri

Damergou- Tanout

Dileram - N'Guigmi

Fara'a - Djoundjou, Dosso, Gaya

Gagaraou - Birnin Kazoé

Gaskia - Zinder

Haddin-Kay - Aguié, Dakoro, Magaria, Tagriss

Kaocen - Arlit

Niyya - Konni

Nomade - Agadez

Rounkondoum - Doumega

Saraounia - Konni, Madaoua, Maradi, Tahoua

Shukurah - Matameye, Zinder

Tambara - FM Tahoua

Tarmamoua - Tessaoua

Té Bon Sé - Tillabéri

 

Ghana:

Zuria FM – Kumasi

 

Senegal:

Radio Dunyaa FM – Tamba