1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani rukunin sojin kiyaye zaman lafiya na Uganda ya isa a Mogadishu

March 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuQC
Wasu karin sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka sun isa a Somalia. A yau wasu jiragen sama biyu dauke da sojoji kimanin 700 na kasar Uganda suka sauka a filin jirgin saman birnin Mogadishu yayin da wasu jiragen sama 3 suka kai kayan aiki da makamai ga sojojin. A dab da isar dakarun kiyaye zaman lafiyar an halaka sojojin gwamnatin Somalia su biyu a wani harin gurnati da ´yan tawayen musulmi suka kai. Kungiyar AU ta yi alkawarin tura sojoji dubu 8 a Somalia. Dakarun kiyaye zaman lafiya zasu kasance kasar ne a karkashin kudurin MDD da nufin kawo karshen rikicin da kasar da ke yankin kahon Afirka.