Wani rikici a birnin Karbala yayi sanadiyar mutuwar mutane 51 | Labarai | DW | 28.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani rikici a birnin Karbala yayi sanadiyar mutuwar mutane 51

Gwamnatin Iraqi ta tura karin dakaru zuwa birnin Karbala a wani yunkuri na shawo kan tashe tashen hankula da suka barke tsakanin dubun dubatan masu ziyarar ibada wadanda suka hallara a birnin don gudanar da bukin daya daga cikin ranaku mafi tsarki a kalendar ´yan shi´a. ´Yan sanda sun ce wasu ´yan bindiga sun kokarin karbe iko a yankin dake kusa da wasu wuraren ibada biyu masu tsarki na ´yan shi´a. Akalla mutane 51 aka kashe yayin da wasu da dama suka jikata a wata musyar wuta da aka yi tsakanin ´yan sanda da kuma ´yan bindigan. Yanzu haka an kafa dokar hana fita yayin da aka umarci masu ibadar da su fice daga yankin.