1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani mummunan rikici ya ɓarke a birnin Kinshasa na Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango, kwana uku kafin gudanad da zaɓe a ƙasar.

July 28, 2006
https://p.dw.com/p/Buos

Wani mummunan rikicin da ya ɓarke a birnin Kinshasa na Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango, ya janyo asarar rayukan ’yan sanda uku. Waɗannan tashe-tashen hankullan dai sun faru ne kwana uku tak, kafin a gudanad da farkon zaɓen dimukraɗiyya a ƙasar a cikin shekaru 40. Wani kakakin Majalisar Ɗinkin Duniya a Kwangon ya ce, magoya bayan tsohon shugaban ’yan tawaye Jean-Pierre Bemba, wanda yanzu ya tsaya takarar zaben shugaban ƙasa ne, suka ta da tarzoma a kan titunan birnin, inda suka cinna wa motoci da dama wuta suka kuma yi ta ƙoƙƙona kantuna da gidaje. Shi dai Bemba yana ɗaya daga cikin ’yan takara 32 da za su tsaya a zaɓen. A halin yanzu dai, an girke dakaru kusan dubu 19 na Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma ƙungiyar EU a ƙasar don su tabbatad da tsaro a lokacin zaɓen.