Wani kwamiti ya yi tir da MDD kan biris da zargin fyade
December 17, 2015Talla
A kalla dai a kwai sojojin Faransa 13 kana biyu daga Equatorial Guinea a yayin da uku 'yan kasar Chadi ne ke da alaka da cin zarafin kana nan yara a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a tsakanin shekara ta 2013 zuwa 2014 a cewar wani rahoton Majalisar Dinkin Duniyar a watan Afrilu.
A binkicen kwamitin na mutane uku sun yi kakkausan suka ga yadda Majalisar Dinkin Duniyar ta yi kan zarge-zargen tare da sukar lamirin wasu manyan jami'an hukumar bisa gazawa domin daukar matakin da ya dace.