1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani kusa a kungiyar al-Qaida ya shiga hannun hukumomin Iraki

February 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9H

´Yan sanda a Iraqi sun cafke mutum na hudu mafi girma a kungiyar al-Qaida dake kasar. Gidan telebijin Iraqi ya rawaito jami´ai na cewa a halin yanzu suna bincike akan ko shugaban kungiyar a Iraqi wato Abu Mussab al-Zarqawi ya tsere zuwa Iran. Wani gajeren rahoto da gidan telebijin din ya bayar ya ce mutumin da aka kama shi ne Mohammed Rabei wanda ake wa lakabi da Abu Dhar. A kuma halin da ake ciki wani babban jami´in tsaron Iraqi ya ce gwamnati na samun wasu bayanai dake nuni da cewa al-Zarqawi ya tsere zuwa Iran bayan wani samame da dakarun Amirka da na Iraqi suka kai a yankin yammacin Iraqi.