Wani kanfanin tsaron Australia ya kashe mutane a Iraki | Labarai | DW | 10.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani kanfanin tsaron Australia ya kashe mutane a Iraki

Jamian wani kanfanin tsaro na kasar Australia a Iraki sun harbe har lahira wasu matan Iraki biyu cikin wata mota a birnin Bagadaza.Yan sanda sunce jamian tsaron da suke gadin wannan tawaga sun bude wuta kann wannan motar inda matan biyu suka rasa rayukansu suka kuma tsere daga yankin.Kanfannin ya amince da wannan laifi ya kuma roki gafara daga gwamnatin Iraki.Kanfanin yace zai kaddamar da bincike hakazalika ya baiyana biyan diyya ga iyalan matan da suka rasa rayukan nasu.Gwamanatin kasar Irakin ta bude wani sabon bincike kann wannan taasa.Yanzu haka dai an fara sa ido kanfanonin tsaro dake aiki a Iraki,bayan harbe harbe da jamian kanfanin Blackwater na Amurka sukayi a watan daya gabata wanda wanda ya kashe mutane 17 a birnin Bagadaza.