Wani jirgin soji na Kwango ya fadi
September 30, 2017Talla
Wata majiya soji ta ce jirgin da ya tashi daga garin Ndolo dauke da fasinja 20 zuwa 30 galibi sojoji da kuma makamai zuwa garin Kivu a gabashin Kwango ya fadi a garin N'sele da ke da nisan kilomta 100 daga Kinsasha. Kuma bisa ga dukkan alamu babu daya daga cikin fasinjan da ke cikin jirgin wanda ya tsira da ransa.