1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani jirgin ruwan fasinjan Masar ya nutse a tekun Maliya

Wani jirgin ruwan fasinjan kasar Masar dauke da mutane fiye da 1,300 ya bace akan tekun maliya.

Jamian kasar Saudiya sunce mai yuwa ne jirgin na dauke da wadanda suka kammala aikin hajjinsu ne daga kasar Saudiya.

Yanzu haka,an gano gawarwakin mutane 15 da wasu 100 da ransu.

Jiragen sama masu saukar angulu da jiragen ruwa na kasashen Saudiya da Masar suna ci gaba da shawagi domin aiki ceto da kuma gano inda jirgin ya nutse

Jamian sunce,jirgin mai suna Al- Salaam 98,ya taso ne daren jiya daga kasar Saudiya,inda ake sa ran isarsa Masar da safiyar yau dinnan amma baa gan shi ba.