Wani jirgin ruwa na yaƙi na Korea ta arewa ya tarwatse cikin teku
March 26, 2010Wani jirgin ruwa na yaƙi na korea ta ƙudu ya tarwatse a cikin ruwan teku a kusa da kan iyaka da Korea ta arewa bayan da wani abu da har yanzu ba a san ko minene ba ya fashe a cikin Ahalin da ake ciki dai rahotanin sun nuna cewa masu aikin agaji sun yi kokarin ceto mutane 58 cikin mutun 104 dake cikin jirgin,yanzu haka dai gwamnatin ta Koreya ta ƙudu ta kira taron gaugawa akan wannan al amari.kanfanin dilanci labarai na kasar korea ta ƙudu Yonhap ya ce jirgin na koreya da farko ya ɓude wuta ne akan wani abin da ke a gabansa da bai tantance ko minene ba,to amma kuma daga bisani an ambato kakakin gwamnatin ya na mai cewa abinda jirgin ya harbi tsuntsya ne da suka tashi.wani babban jami 'i daga fadar gwamnatin ta Korea ta Ƙudu Kim Hye ya ce ba mamaki makobtiyar kasar wato Koreya ta Arewa ta na da hannu a cikin wannan aiki na asha
Mawallafi :Abdourahamane HassaneEdita : Abdulahi Tanko Bala