Wani harin bam ya rutsa da sojojin Turkiyya | Labarai | DW | 17.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani harin bam ya rutsa da sojojin Turkiyya

Akalla sojoji 13 ne suka mutu wasu kuma 48 suka samu raunuka sakamakon wani harin bam da aka kai wa wata bas mai dauke da sojojin da safiyar wannan Asabar din a birnin Kayseri da ke tsakiyar kasar.

Rahotanni daga kasar Turkiyya na cewa akalla sojojin kasar 13 ne suka mutu wasu kuma 48 suka samu raunuka sakamakon wani harin bam da aka kai wa wata motar bas mai dauke da sojojin da safiyar wannan Asabar din a birnin Kayseri da ke tsakiyar kasar.

Cikin wata sanarwa ce dai da ta fitar, rundunar sojojin kasar ta Turkiyya ta ce sojojin da wannan hari ya rutsa da su, sun samu izinin fita ne daga barakin sojoji na musamman. A cikin wani jawabi da ya yi, mataimakin Firaministan kasar Numan Kurtusmus, ya ce shaidu da dama na nuni da cewa shi ma wannan harin 'yan jam'iyyar PKK ne suka kai shi irin wanda suka kai na makon da ya gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 44 a tsakiyar birnin Santambul.  

Bas din dai na wani kamfanin sufuri ne da ke birnin na Kayseri, amma yana dauke da sojojin ne yayin da wata mota da aka dana bam a cikinta ta tarwatse a daidai lokacin da bas din ke wucewa.