1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani hari a yankin Somali na kasar Habasha ya halaka mutane 16

May 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuKW
Hukumomi a kasar Habasha sun ce an kashe akalla mutane 16 sannan an jiya sama da mutum 60 rauni a wasu hare hare da aka kai kan wasu kauyuka biyu dake yankin Somali. Rahotanni sun ce wasu da ba´a gane su suka kai hari kan kauyukan Jijiga da Degah. Da farko wani da ake zargi dan kungiyar ´yanto yankin Ogaden ya jefa gurnati kan masu bukin ranar hutun kasa baki daya. Akalla mutane 10 suka rasa rayukansu sakamakon wannan hari.