Wani dan harin kunan bakin wake ya ta da bam a Iraqi. | Labarai | DW | 30.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani dan harin kunan bakin wake ya ta da bam a Iraqi.

A kasar Iraqi, wani dan harin kunan bakin wake ya ta da bam da sanyin safiyar yau a cikin motarsa, a wani kwalejin horad da `yan sanda a garin Nasiriyah da ke kudancin kasar. Rahotannin da muka samu na nuna cewa, a kalla dan sanda daya ya rasa ransa a harin, sa’annan wasu mutane 39 kuma suka ji rauni, a cikisnu har da sojoji da fararen hula. Harin na safiyar yau dai shi ne na baya-bayan nan, a jerin tashe-tashen hankullan da ake zargin `yan tawayen mabiya darikar Sunni da shiryawa, inda a cikin kwanaki biyun da suka wuce, mutane da dama suka rasa rayukansu, sa’annan wasu kuma ji munanan raunuka.

A wani harin kuma, har ila yau dai a kewayen garin na Nasiriyah, wani sojan kasar Italiya ya ji rauni, yayin da wani bam da aka dasa a gefen titi ya tashi kusa da motar da yake sintiri a cikinta, a gaban sansanin sojin Italiya da ke girke a kasar Iraqin.