Wani bincike da aka gudanar a Iraqi, ya ce kusan ’yan ƙasar dubu ɗari 6 da 50 ne suka rasa rayukansu tun da Amirka ta afka wa ƙasar. | Labarai | DW | 12.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani bincike da aka gudanar a Iraqi, ya ce kusan ’yan ƙasar dubu ɗari 6 da 50 ne suka rasa rayukansu tun da Amirka ta afka wa ƙasar.

Wani binciken da kafofi masu zaman kansu suka gudanar a Iraqi na nuna cewa ’yan ƙasar kusan dubu ɗari 6 da 50 ne suka rasa rayukansu, tun da Amirka ta afka wa kasar da yaƙi a cikin shekara ta 2003 kawo yanzu. An dai gudanad da binciken ne a yankuna 47 da aka zaɓa, waɗanda kuma suka ƙunshi duk fadin ƙasar. Masu gudanad da binciken sun ce sun yi lissafin duk mutuwar da aka yi a wannan lokacin, kama daga waɗanda suka rasa rayukansu sakamamon yaƙin da tashe-tashen hankulla, har ya zuwa waɗanda rashin lafiya da kamuwarsu da cututtuka daban-daban suka janyo mutuwarsu.