1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani badukun da ke kera sassan jiki a Jos

Abdullahi Maidawa daga Jos/ MABJuly 6, 2016

An samu wani matashi dan Najeriya da ke da fasahar kera wasu sassan jikin bil Adama kana yayi dashensu a kan wadanda suka rasa wata gaba ta jikinsu.

https://p.dw.com/p/1JJza
Deutschland Leipzig Prothesen für Hand
Hoto: picture-alliance/dpa/P. Brandstädter

Abubakar Shuaibu Abdullahi Narkuta ne matashin da Allah yayi wa baiwar kera wasu sassan jikin bil Adama, Asalinsa dai baduku ne, amma ya kan kirkiri sassan jikin bil Adama daidai da na kasashen Turai, kuma tasa kan kasance maras nauyi har kasa da kashi 11,bisa 100 idan za'a kwatanta da na kasashen ketare.

Malam Shuaibu ya ce idan ya zo kera hannu, ko yatsun hannu, ya kan auna daya hannun ko yatsun da ke da lafiya domin yayi dashen hannu ko yatsun da aka guntile.

Jama'a daga ciki da wajen Najeriya na zuwa Jos, don dashen gabobin jikinsu, kuma Malam Shuaibu ya ce a shekaru 15 da yayi ya na wannan sana'a, ba ya sanya maganar kudi gabansa. Babban abin da yake hankoro shi ne taimaka wa al'umma ta yadda masu nakasa za su ci moriyar baiwar da Allah yayi masa.

Abubakar Shuaibu Narkuta ya roki samun tallafin hukumomi domin ya samu ci gaban aikinsa da fasahar zamani, da zummar taimaka wa al'umma baki daya