Wani alikoftan Amirka yayi hadari a Afghanistan | Labarai | DW | 06.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani alikoftan Amirka yayi hadari a Afghanistan

Wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojin Amirka ya yi hatsari a Afghanistan. Alikoptan yakin dai ya yi hatsari ne a lokacin da yake kai farmaki. Kawo yanzu ba´a san makoma sojojin Amirka 10 dake cikin jirgin ba, kana kuma ba´a san musabbabin hatsarin ba. To amma rundunar sojin Amirka a Afghanistan ta ce ba abokan gaba suka harbo jirgin ba.