Wani ƙazamin ba ta kashi ya ɓarke a Kwango. | Labarai | DW | 21.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani ƙazamin ba ta kashi ya ɓarke a Kwango.

Wata ƙazamar fafatawa ta ɓarke a ƙasar Jumhuriyar Dimukraɗiyya ta Kwango, tsakanin magoya bayan shugaba Joseph Kabila da abokin hamayyarsa Jean-Pierre Bemba, abin da ya tilasa wa mutane fiye da dubu 2 ƙaurace wa matsugunansu. Jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar sun ce ’yan gudun hijira da dama ne suka yi ƙaura zuwa ɗaya ƙasar Kwangon, wato Kwango Brazaville. A zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a zagaye na biyu dai, shugaba Kabila ne ya sami nasara da kashi 58 cikin ɗari na ƙuri’un da aka ka da, bisa sakamakon da hukuman zaɓen ƙasar mai zaman kanta ta bayar. Amma Bemba ya ƙi amincewa da sakamakon, inda kuma ya ce zai ƙalubalance shi ta hanyar shari’a a kotu.